Macizai da kwadi masu gashi katan-katan da aka kama a Najeriya ashe Turai suka nufa
- Hukumar hana fasakwauri ta kasa ce ta cafke akwatunan halittun ranar 24 ga watan yuli
- Kafin halittun su bar Nigeria an mika su ga jami'ar Uyo na Akwa ibom ne domin u kulawa da su
- Minista ya ce gwamnati ba zata bari kasar nan ta zama mazurarin safarar miyagun halittu ba
Gwamnatin tarayya ta sanar da cewar macizai 104, tsaka, kadangaru, tau-tau, kwadi masu gashi da ragowar wasu muggan halittu da hukumar hana fasakwauri ta kasa ta kama a garin calabar na jihar cross river batan hanya suka yi daga turai a hanyar su ta zuwa kasar Luxembourg.
An shigo da halittun Nigeria ne daga kasar Cameroon a wasu akwatunan katako na musamman a ranar 24 ga watan yuli, amma hukumar hana fasakwauri ta kasa ta yi nasarar cafke su a tashar shige da fice ta cikin ruwa da ke garin calabar kuma ta danka su a hannun hukumar kula da kayayyakin gonar da a ka shigo da su nigeria, wacce ita ma ta mika su hannun ma'aikatar kula da muhalli.
Bayanan farko da muka samu sun nuna cewar an yi nufin shigar da muggan halittun ne zuwa jihar Lagos kafin daga bisani ministan kula da muhalli, Alhaji Ibrahim Usman Jibril, ya bayyana cewar kwarin na hanyar zuwa kasar Luxembourg ne kamar yadda yake rubuce jikin akwatinan da suke ciki sannan kuma ya bayyana kokarin gwamnati na ganin cewar bata bar kasar nan ta zama mazurarin safarar miyagun kwari da dabbobi ba.
DUBA WANNAN: An gano mugun nufin Shekau da Boko Haram
Minstan ya ce "gwamnati na yin kokari na kare kasa da yan kasar nan, kokarin gwamnatin ne ma ya sa hukumar hana fasakwaurin ta gano tare da cafke miyagun halittun" sannan daga bisani ya yi jinjina ga hukumar hana fasakwauri ta kasa a kan wannan nasara da suka samu.
Kafin halittun su bar Nigeria dai an mika su ga jami'ar tarayya da ke birnin Uyo na Akwa ibom ne domin kulawa da su. Da ya ke karbar halittun a madadin jami'ar, Dr. Edem Eniang, na sashen karatun gandun daji da muhalli, ya ce "bisa ga dukkan alamu an yi niyyar safarar halittun ne zuwa Nigeria domin sayarwa, yana mai karin haske da cewar dukkanin halittun masu guba ne kuma akwai wadan da suke cikin irin wannan sana'a ta kiwon muggan halittu domin sayar da dafin su. Ya Kara da cewar dafin maciji na da natukar daraja a kasuwa domin a na amfani da shi wajen hada magunguna na musamman."
DUBA WANNAN: Kungiya ta baiwa Majalisar Dattijai wa'adi, ko su tantance Magu, ko su fuskanci fushin ta
Eniang wanda kwararre ne a kan fannin macizai ya bayyana cewa halittun kan iya zama abinci da yankin Asia a ka nufa da su. Ya Kara da cewa halittun na da matukar daraja kasancewar akwai yawaitar gasar samar da magungunan kashe dafin maciji a kamfanunuwa da sashen karatun kimiyyar hada magunguna musamman a kasashen turai.
Tun asali dai an gano adadin halittun ya kai 600 daga takadar dake dauke da kididdigar yawan su, amma sashen kula da kayayyakin gona da hadin gwuiwar jami'ar ta uyo sun bayyana cewar wasu daga cikin halittun sun mutu a lokacin da suka bude akwatunan domin tantance halittun.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng