Kalubale: Rayuwar kunci ta almajirai, shin wai ina masu kiran kansu dattijan Arewa ne?

Kalubale: Rayuwar kunci ta almajirai, shin wai ina masu kiran kansu dattijan Arewa ne?

- A arewacin Najeriya ne kawai ake almajirci a duk fadin duk duniya, almajirci dai bashi da wani banbanci da cin zarafin yara, rashin sanin nauyin iyayentaka, dama bautar da bil-adama, shin ina dattijan Arewa da malamanta, 'yan siyasarta da shuwagabannin gargajiya?

Ana buga kugen siyasa, zaka ji manyan kasa musamman daga arewa sun fito suna cewa sune iyaye, sune manyan arewa, sune dattijai, amma baza ka ji su a wata muhimmiyar shawara domin waiwayar matsalar almajirci ba.

Sharhi: Rayuwar kunci ta almajirai, shin wai ina masu kiran kansu dattijan Arewa ne?
Sharhi: Rayuwar kunci ta almajirai, shin wai ina masu kiran kansu dattijan Arewa ne?

Kamar wasa, shekaru 200 kenan arewa na harkar almajirci ta ci da habaka, inda babu abun da yaran keyi sai gara-ramba a gari da neman tuwo. Lungu da sakon garuruwan arewa, zaka sami makarantun alarammomi da kan tara almajirai domin karatun kur'ani.

A duk kabilun Najeriya da ke addinin Islama, Hausa/Fulani ne kawai ke watsa 'ya'yansu almajirta. Haka ma kuma duk kasashen duniya da ke Islama, a Najeriya ne kawai ake almajirci.

DUBA WANNAN: An gano me Shekau yake so ya cimma da muguwar akidarsa

Tambaya shine, almajirci addini ne ko al'ada? Menene alfanun almajirci? Shin karatun allo bazai yiwu a gaban iyaye bane? Shin ciyarwa ta iyali a hannun wa take?

Ina shuwagabannin yankin? Ina masarautu dake kashe kudaden jiha? Ina dattijan arewa? Ina malaman addini? Ina 'yan siyasa? Majalisu da na zartaswa? Shin arewa na da makoma kuwa? Hakki a hannun wa yake?

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng