Famanen Sakatare da ake zargi da satar dukiyar kasa ya dawo da biliyoyi ga gwamnati

Famanen Sakatare da ake zargi da satar dukiyar kasa ya dawo da biliyoyi ga gwamnati

- Gwamnatin APC ta ci zabe bisa kokarin yaki da cin hanci da rashawa

- An kama famanan Sakatare da kudaden haram, amma ya dawo dasu

- A ma'aikatar kwadago ya ke aiki

Babbar kotu a jihar Legas, ta kwace wa amanan Sakatare kudadensa har Naira miliyan dari shida da sittin, sannan kuma da dala miliyab dari da arba'in, gami da katafaren gida da wani Otal da ya giggina a jihar Legas.

Famanen Sakatare da ake zargi da satar dukiyar kasa ya dawo da biliyoyi ga gwamnati
Famanen Sakatare da ake zargi da satar dukiyar kasa ya dawo da biliyoyi ga gwamnati

Clement Onubuogo, dai Famanan Sakatare ne a ma'aikatar kwadago da iyar da ayyuka, ya kuma tara wadannan kudade ne a lokacin mulkin Goodluck Jonathan. Kotu dai ta tabbatar da cewa ya kwashi kudaden ne daga kudin shirin you-win, na tallafawa samari.

Alkali Abdulaziz Anka ne ya yanke wannan hukunci, kuma lauyan EFCC Rotimi Oyedepo yayi farin ciki da wannan hukunci. Babu dai wanda yake tsammani Mr. Clement zai iya daukaka kara, ko ma ya iya dawo da kudaden mallakinsa.

DUBA WANNAN: Rigimar Telu fari da Telu baki na neman jawo wa duniya jangwam

An dai bankado badakala da yawa a karkshin ma'aikatann gwamnati a wancan lokacin na mulkin PDP, an kuma kwaci kudade da yawa an mayar lalitar gwamnati, sai dai har yanzu ba'a ji wanni babban barawo ya sami dadadden hukuncin zaman kurkuku ba, ko ma hukuncin rataya saboda munin satarsa.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel