Daga damben yashi, 'yan damben Najeriya sun shilla zuwa gasar dambe ta duniya

Daga damben yashi, 'yan damben Najeriya sun shilla zuwa gasar dambe ta duniya

An zabi shagon Najeriya guda shidda domin su wakilci Najeriya a damben duniya ta 2017, gasa da za'a fara a kasar Faransa.

Daniel Igali, shugaban wasanni da suka shai Rasilin na kasa, ya furta cewa shagon Najeriya shida ne suka cancanci shiga gasar duniya ta dambe ta bana wadda za'a yi a kasar Faranshi. Ya fadi hakan ne a Yenogoa, babban birnin jihar Bayelsa a jiya.

Daga damben yashi, 'yan damben Najeriya sun shilla zuwa gasar dambe ta duniya
Daga damben yashi, 'yan damben Najeriya sun shilla zuwa gasar dambe ta duniya

Mata 4 ne zasu wakilci Najeriyar, maza kuma guda biyu, sai kociyansu guda biyu, a gasar da za'a fara a 20 ga wannan watan, kuma a gama a 27 ga watan na Agusta.

Amas Daniel da John Emmanuel dai hamshakan 'yan dambe ne da suka kama kambu da yawa a baya, a cewa Igali, domin haka baza su bamu kunya ba.

DUBA WANNAN: Sanata Kwankwaso ya ce yana nan daram a APC

Ya kuma bayyana sunan matan da Blessing Obudu, da Adekuroye Odunayo, Mercy Genesis da Aminat Adeniyi, wadanda suma gwarazan 'yan dambe ne, ya kuma ce baza su ba Najeriya kunya ba a idon duniya.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng