Muguwar cuta ta kama samari 15 da suka yi lalata da jaki

Muguwar cuta ta kama samari 15 da suka yi lalata da jaki

- 'Yan shaye-shaye kan far ma dabbobi da lalata

- Akwai mugayen cutuka tattare da dabbobi

- Samarin sha biyar sun shiga halin ni-'ya-su

Samari goma sha biyar ne suka kamu da wata mummunar cuta da ake kira rabies, bayan da suka kama wata macen jaki suka yi ta lalata da ita don dabbanci.

A can kasar Maroko ne dai abin ya faru, a arewacin Afirka, a wani gari mai suna Sidi Al-Kamel a cikin hamada. Shekarun yaran dai bai gaza sha-kaza ba, wada hakan ya nuna basu da cikakken kaifin tunani.

Muguwar cuta ta kama samari 15 da suka yi lalata da jaki
Muguwar cuta ta kama samari 15 da suka yi lalata da jaki

Rahoton dai babbar jaridar Akhbar News Daily ta Morocco ce ta wallafa shi, ta kuma ce iyayen yaran sun kadu matuka, na daya da munin cutar da yaran suka kamu da ita, na biyu kuma da mugunyar halayyar da suka nuna ta bunsuranci.

An garzaya da yaran asibiti na Bekhraa Belksiri domin su karbi magani, hukuma kuma ta baza komarta domin kamo wasu da suma ake tsoron ko sunyi wannan aika-aika.

DUBA WANNAN: Sabbin nade-naden Osinbajo sun biyo baya da kura

Cutar rabies dai kamar ta Ebola take, wato kwayar cutar virus ke kawo ta, ita ma kuma ana daukar ta daga dabbobi ne, musamman mahaukacin kare, bera, jemage da jakkai, kuma tana da wuyar sha'ani, domin har hauka tana jawowa.

Lalata da dabbobi dai na da mummunar illa a kimiyyance, ta fannin kiwon lafiya, domin halitta ta banbanta. A al'adance ma dai jakanta ce mutum ya zub da ajinsa ya taba dabba da bata ji ba bata gani ba.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng