Wani hisabin sai a lahira: Yarinya ýar shekara 10 ta haihu bayan kawunta yayi mata fyaɗe
- Wata karamar yarinya da aka yi a fyade ta haihu
- Kawun yarinyar ne yayi mata fyade sau ba iyaka kamar yadda yarinyar ta fada
Wata karamar yarinya mai shekatu 10 a rayuwa da aka yi ma fyade a kasar Indiya ta haihu a garin Chandigarh na kasar Indiya a ranar Laraba 16 ga watan Agusta, inji rahoton BBC Hausa.
Wannan yarinyar ta haihu ne sakamakon ciki da ta dauka bayan wani yayi mata fyade, sa’annan kotun kolin kasar Indiya ta hana a zubar da cikin yarinyar, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.
KU KARANTA: Anyi artabu tsakanin Sojoji da askarawan Biyafara a Anambra (Hotuna)
Kotun kolin kasar Indiya ta hana a zubar da cikin yarinyar ne sakamakon cewa cikin nata ya tsufa, don haka duk wani yunkurin zubar da cikin zai iya jefa yarinyar cikin hadari.
Sai dai da fari wanann yarinyar bata san tana dauke da ciki ba, inda yan uwanta suka shaida mata cewa wani katon dutse ne a cikinta, don haka ya sanya cikinta girma. Daga karshe ta haihu ta hanyar yi mata aikin tiyata.
A baya ne dai aka ruwaito, labarin wannan karamar yarinya wanda kawunta yayi mata fyade sau ba iyaka a tsawon watanni bakawai da suke tare, amma rahotanni sun tabbatar da ya shiga hannun hukuma.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng