Gidajen haya a Abuja sun yi tashin gwauron zabi

Gidajen haya a Abuja sun yi tashin gwauron zabi

- Gidajen haya a Abuja sun yi tashin gwauron zabuwa

- Akwai kayatattun gidajen haya amma hakan bai sa mutane sun kama ba

- Tsadar rayuwa a yanzu da ake ciki ita ke hana mutane iya biyan kudin haya

A sakamakon koma bayan tattalin arzikin kasa yasa mutane a Abuja da yawa basa iya kama hayar gidaje. Gidaje a Abuja suna kara zama wayam musamman a unguwanni da manya ke zama kamar Maitama, Asokoro, Jabi da Wuse.

Gidajen hayar sun yi tashin gwauron zabuwa, duk da cewa an gina su a kayace bai rinjayi mutanen sun kama hayar su ba.

Gidajen haya a Abuja sun yi tashin gwauron zabi
Gidajen haya a Abuja sun yi tashin gwauron zabi

Wani wakilin gidajen haya Abbas Suleiman ya shaidawa jaridar Daily Trust cewar yawancin gidajen ba a kama bane saboda tsadar da suka yi.

Ya kara da cewa saboda arzikin kasa da ya koma baya shine sanadiyyar mutane da yawa basa iya biyan kudin haya a lokacin da ya kamata.

KU DUBA: Buhari Ya Rubuta Ta'aziyya ga Shugaban Saliyo

Sulaiman ya kara bada misalin wani mutum da ya tashi daga gida mai daki uku ya koma gidan shi da bai karasa ginawa ba saboda tsadar kudin haya kuma ba zai iya biya ba. Har yanzu kuwa gidan da ya tashi ba wanda ya sake kamawa.

Yawancin masu gidajen basu damu ko gidajen da mutane ko babu ba. Saboda suna da gidajen haya da yawa a cikin gari.

Wasu masu gidajen suna bukatar a biya su kudin hayar shekara biyu ne tashi daya, wanda yake yiwa mutane wahala su iya biya a take.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng