Da sallah ta matso sai mijina ya gudu - Wata mata ta kai kara kotu
Wata mata mai suna Risikat Ojo ta kai karar mijinta Mathew Ojo a wata karamar kotu inda ta shaidawa kotun cewa mijin nata yana guduwa da ga gida a duk lokacin da bukukuwan salla suka karato don kawai kar ya kashe masu kudi.
A ranar Talatar da ta gabata ne dai matar ta maka mijin nata a kotun dake zama a garin Agodi na jihar Ibadan inda ta bukaci kotun da ta tilastawa mijin nata ya sake ta tun da wuri kafin lokaci ya kure.
Legit.ng ta samu cewa Risikat Ojo ta shaidawa alkalin kotun cewa: "Tun farko ma dai har yanzu mijin nawa bai biya ni sadaki na ba kuma da zarar salla ta matso to fa ban kasa sa shi a ido na har sai ta wuce da kamar kwana 7 sai kawai ya dawo."
Daga karshe dai alkalin kotun Cif Mukaila Balogon bayan ya gama sauraron duka bangarorin ya yanke shawarar raba auren nasu bayan ya gano cewa tabbas soyayya ta kare a tsakanin su.
Asali: Legit.ng