Manoman tumatir a jihar Kano da Arewacin Najeriya za su dara

Manoman tumatir a jihar Kano da Arewacin Najeriya za su dara

Da yawa daga cikin manoman tumatir sun yanke hukuncin daina noman sanadiyar annoba da ta sauka a bara, amma yanzu sun samu karin karfin gwiwa ta hanyoyi na zamani wajen inganta noman

Bayan irin takfa asarar da annobar wasu kwaruka ta haifar a harkar noman tumatir na shekarar da ta gabata, manoman na jihar Kano sun kara samun karfin gwiwar yin noman tumatitiri mai yawa a daminar bana da ta badi.

Wannan abu ya bayu ne sakamakon sababbin hanyoyi na zamani da ingatattun iri na tumatir da wata cibiyar kasar Turai mai zaman kanta, TechnoServe tare da hadin gwiwar wani kamfanin Syngenta Agro Limited su ka gabatar wa manoman.

Manoman wanda da yawa daga cikinsu, sun hakura da noman tumatir tare da misanya shi da noman wasu amfanin na gona, sanadiyar irin tafka asarar da su ka yi, sun nuna yajewar su da mika kawunan su ga wannan sababbin tsare-tsare da hanyoyi na zamani wajen noman tumatir.

Manoman tumatir a jihar Kano da Arewacin Najeriya za su dara
Manoman tumatir a jihar Kano da Arewacin Najeriya za su dara

Wani manomin kauyen Rimin Dako, Alhaji Shehu Yahaya na karamar hukumar Bagwai dake jihar Kano ya ce, kafin zuwan wannan sabon tsarin na noman tumatir, da yawa daga cikin manoman sun yanke hukuncin ba za su kara noman tumatir ba saboda irin matsalolin da su ka fuskanta a bara.

Ya ce, “a noman bara, na yi shukar tumatir a gonaki har guda biyar, amma ba bu ko gona daya da na samu na mayar da kudin da na kasha wajen noman ballamta kuma wata riba sanadiyar annobar da ta afkawa tumatir a bara.”

Wani manomin shi ma na garin Marga, Mallam Hussaini Ardo,dake karamar hukumar Bichi a jihar ta Kano, Ya bayyana cewa rashin fadakarwa da wayar da kai akan ingatattun hanyoyin zamani da tsare-tsare ne ya haifar mu su da matsaloin da su ka fuskanta a bara.

KU KARANTA: Kiwon Lafiya: Dalilai da za su sanya kara riko da abarba

Yana rokon wannan cibiya ta TechnoServe tare da hadin gwiwar kamfanin Syngenta, da su yi azamar samar da kayan harkar noma kama daga ingatattun iri na shuka, takin zamani da magunguna domin gujewa wannan matsaloli da su ka dade su na fama da su.

Shi kuwa shugaban wannan cibiya ta TechnoServe, William Warshauer, ya jaddadawa manoman cewa, cibiyar ta su ta tsaya tsayin daka domin kawowa manoma hanyoyi da tsare-tsare wajen magance mu su matsalolin su.

Ya ce, a halin yanzu cibiyar ta su ta tallafawa kananan manoma 650, 000 wajen habaka noma a cikin jihohi 18 na Arewacin Najeriya.

Don shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng