Ya gima ramin mugunta, daga ƙarshe ya faɗa: Karanta labarin wani Ɗan-Achaɓa maci amana

Ya gima ramin mugunta, daga ƙarshe ya faɗa: Karanta labarin wani Ɗan-Achaɓa maci amana

A ranar Talata 15 ga watan Agusta ne aka gurfanar da wani dan Achaba mai shekaru 28 gaban wata kotun majistri dake garin Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Jami’an Yansanda ne suka tasa keyar dan achaban mai suna Taiwo Adeleke kan tuhumarsa da ake yi da arcewa da babur din Maigidansa bayan an bashi ita ya dinga aikin achaba yana kawo balas.

KU KARANTA: Yara manyan gobe, anya kuwa? Duba halin da ɗaliban jihar Zamfara ke ciki (Hotuna)

Kamfanin dillancin labaru, NAN ta ruwaito dansanda mai kara Olalekan Adegbiti yana fadin dan achaban Adeleke ya gudu da babur din, inda ya kwashe kwanaki ana nemansa ba’a ganshi ba.

Ya gima ramin mugunta, daga ƙarshe ya faɗa: Karanta labarin wani Ɗan-Achaɓa maci amana
Yan achaba

Shi mai babur din, Jelili Moradeyo ya shaida ma kotu cewa darajar babur dinsa ya kai N120,000, kuma shi ya Adeleke babur din ne da nufin zai dinga kawo masa balas a kullum, kamar yadda suka shiga yejejeniya a tsakaninsu.

Asirin Adeleke bai tashi tonuwa ba sai a ranar 11 ga watan Agusta, inda tsohon maigidansa Moradeyo ya hange shi yana tuka wata babur ta daban, bayan an kwashi watanni da dama yana nemansa, nan da nan ya gayyaci yansanda suka kama shi.

Sai dai Adeleke ya musanta aikata laifin, inda daga nan sai alkaliyar kotun Patricia Adetuyibi ta bada belin wanda ake tuhuma akan kudi N120,00 tare da masu tsaya masa guda biyu.

Daga karshe kuma mai shari’a Adetuyibi ta dage sauraron karar zuwa ranar 19 ga watan Satumba, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Wani kasa zaka so ace kake?

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng