Dangote zai gina kamfanin suga da na shinkafa a arewacin Najeriya

Dangote zai gina kamfanin suga da na shinkafa a arewacin Najeriya

A yau ne dai ake sa ran kamfanin nan na Dangote zai sa hannu akan wata yarjejeniyar amincewa tare da gwamnatin jihar Neja wadda zata bude hanya wajen kudurin sa na gina manyan kamfanonin suga da shinkafa a jihar.

Shugaban tsare-tsare na kamfanin Dangote Dakta Mansur Ahmad wannda shine kuma ya wakilci shugaban kamfanin na Dangote Alhaji Aliko Dangote ne ya bayyana hakan a ganin Minna babban birnin jihar Neja.

Dangote zai gina kamfanin suga da na shinkafa a arewacin Najeriya
Dangote zai gina kamfanin suga da na shinkafa a arewacin Najeriya

Legit.ng ta ta samu cewa Dakta Ahmad ya bayyana cewa kamfanin na su yana da sha'awar kafa wani katafaren kamfanin gyaran shinkafa a jihar da zai rika gyara shinkafar da ta kai tan 200,000 a shekara.

Haka ma dai ta bangaren suga kuma, Dakta Ahmad ya bayyana cewa Dangote zai gina wani karin katafaren kamfanin suga da zai rika sarrafa rake da yakai eka 30,000 wajen yin sugan da yakai tan 500,000 duk dai acikin jihar kuma cikin shekaru 3 masu zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng