Dandalin Kannywood: Gaskiyar abunda ke tsakani na Nazir Ahmad - inji Hadiza Gabon

Dandalin Kannywood: Gaskiyar abunda ke tsakani na Nazir Ahmad - inji Hadiza Gabon

Shahararriyar yar fim din nan ta masana'antar Kannywood watau Hadiza Aliyu wadda aka fi sani da Hadiza Gabon ta fito fili ta nesanta kanta da wasu maganganu da akeyi mata na cewa tana soyayya da mawakin nan na Hausa watau Nazir Ahmad.

Shahararriyar yar fim din dai Hadiza ta yi wannan bayanin ne a wani dan karamin shiri da ta shirya ma masoyanta a shafin ta na sada zumunta na Instagram inda ta ba masoyan ta dama su tambayeta duk tambayar da suke da ita ita kuma ta basu amsa.

Dandalin Kannywood: Gaskiyar abunda ke tsakani na Nazir Ahmad - inji Hadiza Gabon
Dandalin Kannywood: Gaskiyar abunda ke tsakani na Nazir Ahmad - inji Hadiza Gabon

Legit.ng ta samu cewa a wannan lokacin ne tambayoyi daga masoyanta na ta shigowa sai wani ya tambaye ta gaskiyar maganar da yake ji na yawo a masana'antar na cewa tana soyayya da mawakin inda kuma ta ce ba gaskiya ba ne.

A cikin firar ma kuma dai an tambaye ta asalin ta inda ta bayyana mahaifiyar ta a matsayin yar asalin garin Mubi da ke Adamawa sai kuma baban ta dake dan asalin kasar Gabon.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng