Yadda Boko Haram ta afka ma ƙauyukan Wanori da Amarwa (Hotuna)
- Mayakan Boko Haram sun sake kai hari wasu kauyukan Borno
- Kauyukan da harin ya shafa sun hada da Wanori da Amarwa
Mayakan Boko Haram sun sake kai farmaki a wasu kauyukan jihar Borno guda biyu da suka hada da Wanori da Amarwa wadanda basu wuce kimanin tafiyar mintuna 20 ba zuwa garin Maiduguri.
Wani ma’abocin shafin Facebook Kabir Mohammed Wanori, kuma mazaunin garin ne ya bayyana haka a shafinsa na Facebook, inda ya daura hotunan wasu daga cikin barnar da mayakan Boko Haram suka janyo a kauyukan.
KU KARANTA: Hattara gwamna El-Rufai: Wani mutum na amsar N20 kulllum daga hannun ýan ta’alla da sunan haraji (Hotuna)
Majiyar Legit.ng ta shaida cewa da misalin karfe 10 na daren Asabar ne yan ta’addan suka afka ma kauyukan, inda suka kai har karfe 11:30 sun cin karensu babu babbaka.
Majiyar ta kara da cewa yan ta’addan sun hallaka mutane hudu tare da raunata wasu mutane guda biyu.
A yan kwanakin nan an cigaba da samun dauki ba dadi tsakanin yan Boko Haram da Sojojin Najeriya tun bayan wani umarni da mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya baiwa manyan hafsoshin Sojin kasar.
Umarnin kuwa shine dasu tattara inasu inasu su koma can jihar Borno don gane ma idanunsu halin da ake ciki.
Ga sauran hotunan a nan:
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Kalli matsalar da Boko Haram ta janyo ma Borno:
Asali: Legit.ng