Bugun zuciya ya kama mijin wata mata sanadiyar keta ma sa haddi

Bugun zuciya ya kama mijin wata mata sanadiyar keta ma sa haddi

Bugun zuciya ya kama wani mutum, Udemeh Ukarette, mai shekaru 34, a yayin da ya kama matar sa, Joy Ukarett da wani kwastoman ta wani otel

Shekarun Udemeh da Joy 16 da aure amma ba su samu haihuwa ba, inda ta ce tayi hakan saboda ta samu ciki tunda shi mijin na ta ya kasa.

Jaridar PM EXPRESS ta ruwaito cewa, wannan abu ya faru ne a layin Toyin Giwa na yankin Afonka Shasha da ke jihar Legas.

Bugun zuciya ya kama mijin wata mata sanadiyar keta ma sa haddi
Bugun zuciya ya kama mijin wata mata sanadiyar keta ma sa haddi

Jaridar ta ce, Joy ta sanar da mijinta kuma ya aminta kafin ta kwanta da wannan kwastoman na ta, inda abin ya juya ta fara jin dadin tarayyar su shine ta cigaba.

Da Udeme ya ce ta yanke alakar ta da wannan mutumin shine ta bayyana mijin ba za ta daina ba kuma ta ce mutumin shine babban kwastoman ta sannan ta yi ikirarin idan ya matsa ma ta za ta raba auren su ta komawa daduron ta.

KU KARANTA KUMA: Amfanin ruwan kokwamba guda 5 a jikin dan Adam

Udemeh da Joy wanda 'yan asalin garin Anan ne na jihar Akwa Ibom sun bayyana cewa, sun nemi magani na asibiti da na gargajiya amma har yanzu ba wani labari.

Udemeh ya kai karar matar sa kungiyar su ta 'yan Akwa Ibom a cibiyarsu ta jihar Legas, inda aka yi kokarin a sulhunta amma Joy ta yi mursisi akan ba za ta yanke alaka da sabon saurayinta

Sai dai ta amince za ta cigaba da zama a matsayin matar Udemeh kuma tana tarayya da saurayin na ta.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a email dinmu na labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng