Kwarmato: 'Yadda likitoci suka kashe min mata ta - Auwal Sani
- Sun yanke mata mahaifa ba tare da sanar da ita ko mijinta ba
- Ta kamu da cutar yoyon fitsari da mutuwar barin jiki kafin mutuwar ta
- Mahukuntan asibitin sun nemi su bani kudi a kashe maganar
Likitocin wani Asibitin Kudi dake cikin garin Kaduna sun yankewa wata mata mahaifa wanda wai hakan ya jawo mata yoyon fitsari daga nan sai mutuwar barin jiki kafin daga bisani ma tace ga garin ku nan.
Mijin matar mai suna Auwal Sani ya bayyana cewa ya kai matar sa mai suna Nadiya Sani asibitin lokacin da zata haihu amma sai likitocin asibitin suka dinke mata mahaifa ba tare da sun sanar da ita ko mijin nata ba.
Bayan sun koma gida sai jini ya tsike wa matar daga nan kuma sai suka sake komawa Asibitin don sake ganin likita amma wai da likitocin suka fahimci asiri zai tonu kawai sai suka yanke mahaifar suka jefar.
KARANTA KUMA: Obasanjo ya zayyana dalilan da suka hana soji hambaras da gwamnati
'Lokacin da suka yanke mahaifar ashe sun yanke mata har da blada wanda wai hakan kuma ya jawo mata Yoyon fitsari daga nan sai ta kamu da mutuwar barin wanda daga baya rai yayi halinsa', mai gidan nata ya fadi.
Mijin Nadiya , Malam Auwal Sani Filamba ya cigaba da bayyanawa cewa, sau uku mukarraban Asibitin suna kiran shi suna lallabar shi akan yayi shiru da maganar zasu bashi naira dubu dari biyu amma yaki yarda.
DUBA WANNAN: Magu ya koka, yace manyan barayi na kai masa farmaki
'Nadiya 'yar kimanin Shekaru 38 ta rasu tun a ranar uku ga watan daya na wannan shekarar 2017. Kafin rasuwar ta, tayi kuka da idon ta inda ta bukaci in bi mata hakkin ta', a fadin mijin nata.
"Yanzu muna Kotu amma Shari'ar sai yawo ake yi da ita saboda bani da kudi kuma bani da kowa, don Allah Yan'uwa na idan da yadda wani zai iya taimaka mun wajen ganin an bi min hakkina, ina neman taimako." a fadin Auwal miji ga marigayiya Nadia.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a email dinmu na labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng