Rayuwar dalibai 2 na jami'ar Legas ta salwanta a gobarar wani Otel a jihar

Rayuwar dalibai 2 na jami'ar Legas ta salwanta a gobarar wani Otel a jihar

Shi ajali aka ce baya wuce ranarsa domin wasu daliban jami'ar Legas sun riga mu gidan gaskiya sanadiyar gobarar wani otel a jihar

Dalibai biyu na Jami'ar Legas (UNILAG) sun mutu a cikin wata gobara da ta kama a tsakar dare a wani otel na Legas.

Wadanda tsautsayin ya shafa sun mutu bayan kwanaki kadan da konewar da su ka samu sanadiyar gobarar.

Duka daliban biyu, Roli Odugwu, 'yar aji biyu mai karantar aikin jarida da Linda Elegeonye, 'yar aji uku da ta ke karanatar ilimin dokoki mazauna unguwar Fagunwa ne dake jihar ta Legas.

Rayuwar dalibai 2 na jami'ar Legas ta salwanta a gobarar wani Otel a jihar
Rayuwar dalibai 2 na jami'ar Legas ta salwanta a gobarar wani Otel a jihar

Rahotanni daga jami'ar sun bayyana cewa, daliban sun fita wani sha'ani ne da za ayi a wajen makarantar, a yayin da su ka ga dare ya yi mu su kuma ba damar dawowa makaranta shine suka kama hayar otel na dare daya.

Wata kawar Roli, da taki bayyana sunanta, ta ce Roli ta bayyanawa mahaifiyarta cewa za su yi hayar otel din na dare daya.

KU KARANTA KUMA: Amfanin ruwan kokwamba guda 5 a jikin dan Adam

Wadanda azal din ta afkawa su na bacci gobarar ta kama sanadiyar lalacewar wata na'ura mai sanyaya daki, kuma abinka da dare ba a kawo mu su dauki da wuri ba.

An garzaya da su babban asibitin Gbagada, inda a ranar asabar din da ta gabata da misalin karfe 4 na asuba Roli ta cika kuma an binne ta a makabartar Atan dake unguwar Yaba ta jihar Legas

Jim kadan bayan mutuwar Roli ne , aka samu rahoton cewa itama Linda ta ce ga garinku nan bayan kwanaki shida da ta shafe ba ta hayyacin ta.

Don shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng