Dambazau ya ce Nnamdi Kanu ya ruguza ka'idojin belinsa da kotu ta bashi

Dambazau ya ce Nnamdi Kanu ya ruguza ka'idojin belinsa da kotu ta bashi

- An kama Nnamdi Kanu kan kokarinsa na tada fadan kabilanci a 2015

- An sake shi bisa sharudda guda goma

- Ya dai karya dukkan wadannan sharudda amma hukumomi sun yi biris

Ministan harkokin cikin gida, Laftanal Janar Abdurrahman Bello Dambazau (murabus) ya zargi shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu da Saba sharrudan belli da kotu ta gindaya mass.

Dambazau yayi zargin ne a wata hira da yayi da manema labarai a ofishin sa da ke Abuja, ya kara da cewa kotu ne ke da daman yanke masa hukunci tunda ita ne ta bada bellin nasa tun farko.

Dambazau ya ce Nnamdi Kanu ya ruguza ka'idojin belinsa da kotu ta bashi
Dambazau ya ce Nnamdi Kanu ya ruguza ka'idojin belinsa da kotu ta bashi

Amma duk da haka yace ba dalili bane yan sanda su tsare shi a yanzu tunda lokacin komawa kotu domin ci gaba da shari'ar sa baiyi ba. Ministan yace "Hakikanin gaskiya Nnamdi Kanu ya saba sharrudan bellinsa amma lokacin komawa kotu domin ci gaba da shari'ar sa bai yi ba, mu muna ganin ya saba sharudan bellinsa, ya rage ma kotu ta tabbatar da hakan ko akasin hakan.

"A yanzu dai yan sanda baza su je su kama shi ba, domin ya saba ma sharrudan bellinsa, Kanu zai sake gurfana a gaban kotu kuma zasu tabbatar ko ya saba sharudan belin". Inji Ministan

DUBI WANNAN: Tsoron Ali Gusau ya saka Yarima yin sharia a Zamfara

Ministan kuma yayi tsokaci akan dalilan da yasa gwamnatin tarayya bata tsare samarin arewa da suka baiwa kabilar ibo wa'adin barin arewa ba, yace rundunar yan sandan sirri na DSS ta gayyace su kuma ta tattauna dasu amma baiyi bayanni akan tattaunawar da akayi dasu ba.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a email dinmu na labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng