Hattara gwamna El-Rufai: Wani mutum na amsar N20 kulllum daga hannun ýan ta’alla da sunan haraji (Hotuna)

Hattara gwamna El-Rufai: Wani mutum na amsar N20 kulllum daga hannun ýan ta’alla da sunan haraji (Hotuna)

A ranar Juma’a 11 ga watan Agusta ne aka hangi wani matashi mai matsakaicin shekaru yana cin zalin wasu kananan mata yan talla, kamar yadda Legit.ng ta gano.

Shi dai wannan matashi da ba’a tantance sunan shi ba har zuwa lokacin shirya wannan labara ya yi kaurin suna ne wajen amsan Naira 20 daga kowacce yar talla dake kan titin Samarun Zaria, kamar yadda aka hange shi yana yi.

KU KARANTA: Rundunar Ýansanda ta yi caraf da wasu masu yankan kai a Legas (Hotuna)

Da dama daga cikin yan tallar kananan yara ne mata dake siyar da su masara, gyada, aya da sauransu, kuma sun bayyana cewa a kullum idan sun fito yawon talla, sai wannan matashi ya amshi N20 daga hannunsu da sunan wai harajin gwamnati ne.

Hattara gwamna El-Rufai: Wani mutum na amsar N20 kulllum daga hannun ýan ta’alla da sunan haraji (Hotuna)
Matashin a bakin aiki

Sai dai abin tambaya a nan, shine shin gwamnatin jihar Kaduna tare da hukumar karbar haraji ta jihar na sane da aikin baban giwa da wannan matashi ke yi?

Hattara gwamna El-Rufai: Wani mutum na amsar N20 kulllum daga hannun ýan ta’alla da sunan haraji (Hotuna)
Matashin a bakin aiki

Ya zama dole a tambayi gwamnati sakamakon gwamnatin tayi ikirari an daina biyan kudin haraji hannu da hannu kamar yadda wannan matashi ke yi, don haka ya dace ta bincika kada ya zamana tayi shiru ana zaluntar masu karamin karfi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Wani mai garkuwa da mutane ya sha da kyar, kalla:

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng