Dalilin daya sa soji basu yi juyin mulki ba tun shekarar 1999 - Obasanjo

Dalilin daya sa soji basu yi juyin mulki ba tun shekarar 1999 - Obasanjo

- Tsohon shugaban kasan Najeriya, Olusegun Obasanjo yayi bayani akan dalilan da yasa soji basu yi juyin mulki ba a kasar Najerriya tun shekarar 1999.

- Mista Obasanjo yayi bayanin ne a bukin kaddamar da wata littafi da akayi ma lakabi da “Making Africa Work” a unguwar Victoria Island a legas.

Marabutan littafin sun hada da tsohon shugaban kasa Obasanjo da kuma wasu mutane guda uku – Greg Mills, Direktan gidauniyar Brenthurst; Jeffrey Herbst, shugaban NEWSEUM da kuma Dickie Davis, wani tsohon Manjo Janar mai murabus.

Mr. Obasanjo ya mulki Najeriya a lokacin mulkin soji a tsakanin 1976 – 1979, daga bayan ya mulki kasar a lokacin mulkin demokridiya daga 1999 – 2007.

Dalilin daya sa soji basu yi juyin mulki ba tun shekarar 1999 - Obasanjo
Dalilin daya sa soji basu yi juyin mulki ba tun shekarar 1999 - Obasanjo

A cewar tsohon shugaban kasan, juyin mulki da soji sukayi ya kawo koma baya sosai a habakar demokradiya, harkan mulki da kuma hadin kan kasa amma duk da haka, haramta juyin mulkin a kudin tsarin mulkin kasa ba shine zai kawo mafita ba.

“Juyin mulki cin amanan kasa ne kuma hukuncin sa shine kisa amma fa idan anyi nasara, wanda yayi juyin mulkin zai zama shugaban kasa. Tabbas, wannan mumunan al’ada ce da ka iya kawo tabarbarewan aikin soji,” Cif Obasanjo ya rubuta.

A yayinda yake bayanin yadda da kawar ta aukuwa juyin mulki a zamanin mulkinsa na farin hula, Mista Obasanjo ya bayyana yadda cikin dabara yayi ma manyan hafsin soji murabus na dole.

“Bayan na hau kujerar mulki, akwai wata hikima da nayi. Na bada umurnin soji su bani sunayen dukkan soji da suke da hannu wajen yin juyin mulki a baya ko kuma wadanda suka amfana da juyin mulkin , misali wandanda aka nada gwamnoni da ministoci, “ tsohon shugaban ya rubuta.

“Tunda basu san mai zanyi da sunayen ba, sun rubuta duka sunayen guda 93 suka mika min. Sai nayi amafani da matsayina na shugaban kasa kuma babban kwamandan hafsoshin Najeriya duk nace suyi murabus a cikin awanni 6, kuma su bar barikin soji a daren juma’a idan ko ba haka ba zasu fuskanci hukunci."

DUBA WANNAN: Fadar shugaban kasa ta dakile damar mace tilo a hukumar zabe ta INEC

“A ranar litinin, marabus dinsu ya tabbata. A yadda nake dubban abin a matsayina na tsohon soja da yayi yaki kuma yayi nasara, nasan cewa duk sojin da aka tube masa kakinsa kuma aka kore shi daga barikin soji kamar kifi ne da ake fidda daga ruwa, dole duk wani karfi da iko da suke dashi ya dushe.

“Darasin da na nuna wajen yi musu murabus din shine, duk daren dadewa, wanda yayi juyin mulki ko ya amfana da juyin mulkin sai ya haddu da hukunci har idan yana raye,” inji Obasanjo.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a email dinmu na labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng