Wani jami’in Soja ya umarci wata mata tuɓe kayanta akan ta sa kayan Sojoji (Hoto)
Wasu rahotanni sun tabbatar da labari inda wani jami’in Soja ya tursasa ma wata mata yin tsirara bayan ya kamata tana sanye da kayan sarki irin na Sojoji akan hanyar ta na zuwa biki.
Sai dai zuwa yanzu ba’a tantance su wanene wadannan jami’an Sojoji da suka cika ma wannan mata mutunci ba, saboda daya daga cikinsu ya rufe fuskarsa da hularsa, dayan kuma bai bari kyamara ta dauke shi ba.
KU KARANTA: Rundunar Ýansanda ta yi caraf da wasu masu yankan kai a Legas (Hotuna)
Legit.ng ta ruwaito anyi ta samun cecekuce da korafe korafe daga yan Najeriya da dama bayan bayyanar hotunan wannan mata, inda dayawa daga cikin mutane ke sukar lamirin Sojojin.

Amma fa tabbasa dokar Najeriya ta hana wani ko wata sanya kayan sarki na kowanne irin hukumar tsaro, musamman na Sojoji, sai dai jama’a da dama sun daura ma kansu sanya kayan Sojoji don nuna isa.

Ko a kwanakin bayan wani bidiyo ya bayyana inda wani babban mutum me kuka yana rokon Sojoji da su yi masa aikin gafara bayan sun kama shi yana sanye da kayan Soji.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Kada a maimaita yakin basasa, Inji tsohon soja, kalla:
Asali: Legit.ng