Sanata Isah Hamma Misau ya shirga mana karya - Hukumar ma'aikatan yan sanda
Hukumar nan ta gwamnatin tarayya da ke kula da harkokin rundunar yan sanda ta musanta maganar da shugaban kwamitin majalisar dattijai a kan harkokin sojin ruwa Sanata Isah Hamma Misau yayi na cewa hukumar na karbar cin hanci kafin yi wa dan sanda karin girma.
Sanata Isah Hamma dai ya shaidawa majiyar mu ne tun farko cewa wani wanda yayi wa farin sani a aikin dan sandan ne ya fada masa cewa sukan bada har kudin da suka kai Naira Miliyan biyu da rabi kafin ayi masu karin girma.
Legit.ng kuma sai daga baya ta samu labarin cewa jami'in hulda da jama'a na hukumar dai Ikechukwu Ani daga bisani ya karyata wannan ikirarin inda yace babu kanshin gaskiya a ciki.
Mista Ikechukwu ya fada wa majiyar mu cewa yadda suke aikin su shine shugaban rundunar yan sandan ta kasa yakan gabatar masu da sunayen wadanda yake ganin sun cancanci karin girma ne su kuma sai su duba su amince.
Asali: Legit.ng