Game da daukar ma'aikata! Ma'aikatar NNPC tayi karin haske tare da gargadi
Ma'aikatar nan ta gwamnatin tarayya dake da alhakin kula da albarkatun man fetur ta kasa watau Nigerian National Petroleum Corporation (NNPC) a turance ta fitar da sanarwa tana mai kara jaddada wa mutane cewa ita fa bata fitar da wata sanarwar daukar aiki ba a halin yanzu.
Wannan kiran na hukumar ta Nigerian National Petroleum Corporation (NNPC) na zuwa ne a dai dai lokacin da ake ta kara samun wasu bayanan karya da aka ce daga hukumar ne suke dada kara yawo a kafafen sada zumunta.
Legit.ng ta tsinkayi jami'in hukumar dake magana da yawunta Mista Ndu Ughamadu yana bayyana cewa takardar da take yawon da kuma take dauke da sa hannun jami'an hukumar ta karya ce don haka mutane su kula kada su faa a tarkon yan damfara.
Mista Ndu ya kuma ce yan Najeriya su kwantar da hankalin su don kuwa idan hukumar zata dauki aiki to zata yi shela ta kafafen sadarwar da suka dace sannan kuma za'ayi gaskiya a cikin shirin.
Asali: Legit.ng