Dandalin Kannywood: Jarumi Aminu Momo ya caccaki sabbin yan fim

Dandalin Kannywood: Jarumi Aminu Momo ya caccaki sabbin yan fim

A wata fira da gogagge kuma jajirtaccen jarumin wasannin fina-finan Hausa na Kannywood watau Aminu Sharif wanda aka fi sani da Momo ya caccaki sabbin fina finan hausan da ake yi yanzu inda ya bayyana su a matsayin soki burutsu da suka rasa ma'ana da kuma nishadantar wa kamar na da.

Jarumin yayi wannan ikirarin ne a lokacin da yake fira da majiyar mu da ta tambaye shi ko yaya zai kwatanta fina-finan da ake yi a masana'antar a yanzu da kuma fina-finan da aka yi a da.

Dandalin Kannywood: Jarumi Aminu Momo ya caccaki sabbin yan fim
Dandalin Kannywood: Jarumi Aminu Momo ya caccaki sabbin yan fim

Legit.ng ta samu dai ya kada baki yace: "To a hakikanin gaskiya dai ba za'ace ba'a samu ci gaba ba musamman ma ta fannin kayan aiki da kuma yadda ake shirya fim din. Yanzu jarumai da sauran masu ruwa da tsaki duk suna yin sana'ar ne da ilimi ba kamar da ba."

"Sai dai kuma idan aka koma a bangaren labaran fina-finan yanzu za a samu cewa ba su da ma'ana kuma da yawansu basu wani ilmantar wa kamar na da din." Ya ce.

Asali: Legit.ng

Online view pixel