Atiku ya mai da martani akan hotunan sa da aka fitar yana cin abinci da yan mata

Atiku ya mai da martani akan hotunan sa da aka fitar yana cin abinci da yan mata

-Na dauke hotuna ne saboda nuna mahimacin yan gudun hijra

-Naci abinci da iyayen su dan na nuna musu abincin na da kayu

-Bai kamata mutane su rika izgilanci da hotunan ba

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya mayar da martani akan hoton sa da ake yadawa a lokacin da yake cin abinci tare da yan mata, a wani taro da ake zargin kamfen yakeyi na zaben 2019.

An fitar da hotuna ne a ranar Alhamis wanda ya nuna tsohon mataimakin shugaban kasan yana cin abinci da yan mata.

Atiku ya mai da martani akan hotunar sa da aka fitar yana cin abinci da yan mata
Alhaji Atiku Abubakar

Atiku ya musanta zargin da ake masa na cewa an dauki hotunan saboda kamfen, yace an dauki hotunan tun shekara 2015 a Yola lokacin da yake kaddamar da kwamatin ciyar da yan sansanin gudun hijira.

KU KARANTA: Boko Haram: Mutane 279 ne suka mutu a maso gabashin arewa a watan Yuli

Yakara da cewa “Hotunan an dauke su ne saboda nuna mahimacin yan gudun hijra, bai kamata a rika izgilanci da hotunan ba

Ya rubuta cewa: ”An dauki hotunan ne shekara biyu da suka wuce, dan ciyar da yan gudun hijira a Yola. Naci abinci tare da iyayen yaran dan na nuna musu Abincin yana da kyau."

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a email dinmu na labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng