Yadda Yariman Bakura na Zamfara ya kusa ruguza Najeriya - Cif Obasanjo
- 'Yadda Yerima ya kusa ruguza Najeriya' Obasanjo
- An faro shari'a a lokacin 1999-2000
- Najeriya na tafiya a tsarin dimokuradiyya ne
A sabon littafi da shugaba Obasanjo ya taya mutum uku wallafawa, mai suna 'Making Africa Work' wanda aka saki a makon jiya, shugaban ya bayyana batun shari'ar Islama da Yeriman Bakura Ahmed Sani ya kaddamar a 1999 a matsayin babban kalubale da ya fuskanta a lokacin mulkinsa.
A cewar shugaba Obasanjon, dama dai can akwai shari'ar a kananan kotuna, wadanda suke kula da sabgar aure, gado, da kananan rigingimu na al'ada a kasar nan, amma a cewarsa, laifuka manya ba'a hukunta su a kotunan sharia, sai da Yariman ya kawo tsarin.
A dai rigingimu da suka biyo bayan wannan kokari na Ahmed Yerima, dubban mutane sun rasa rayukansu, musamman a jihohin Kano, Kaduna, Bauchi da Filato, jihohi masu jama'a kamar zubin Najeriya, musulmi da kirista.
Wannan kuma shi ya sanya kungiyoyi na addini da malamai suka kara daga murya kan batun bukatar sharia, wanda har ya kai arewa da shiga matsalar Boko Haram, masu so a kori tsarin mulki a kawo na addinin Islama ga kowa.
DUBA WANNAN: Shugaba Buhari ne zai lashe zaben shugaban kasa a 2019
A cewar Obasanjo dai, ba domin Allah ne Yeriman ya kaddamar da Shari'ar ba, a'a, wai rigimar sa ce da tsohon shugaban hukumar NSA Ali Muhammad Gusau, wanda yaso bincikarsa yayin da ya kayar da nasa dan takarar a 1999, shi kuwa ya fara bincikar yadda ya sami dukiyarsa.
'Nayi kokarin sulhunta su, kai har tafiye-tafiye na nake hadawa tare dasu zuwa kasashen waje, domin in shirya su, amma abin yaki, wannan shi ne yasa Yerima daukar mataki wanda zai saka shi ya kasa tabuwa daga hukumomi, sai kawai ya kaddamar da shari'ar musulunci a Zamfara' Fadin Obasanjo.
Yariman Bakura dai yana matsayin Sanata ne a yanzu, a jam'iyyar APC, ya kuma taba tsayawa takarar shugaban kasa, yakan kuma jawo cece-kuce kan batutuwa musamman kan shari'a da yadda Boko Haram ta yi asali.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a email dinmu na labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng