Gwarazan Sojojin Najeriya da suka sami karramawa daga Janar Buratai

Gwarazan Sojojin Najeriya da suka sami karramawa daga Janar Buratai

- Yaki da Boko Haram dai yaki ci yaki cinye wa

- An kara wa wasu sojoji mukami saboda jarumtar su

- Janar Buratai ne ya shugabanci bikin

Shugaban rundunar sojojin Nigeria, laftanal janar TY Buratai, ya karrama wasu manyan sojoji guda 2 da ragowar wasu kananun sojoji 151 na runduna ta 21 dake yaki da 'yan kungiyar Boko Haram a jihar Borno

Gwarazan Sojojin Najeriya da suka sami karin matsayi daga Janar Buratai
Gwarazan Sojojin Najeriya da suka sami karin matsayi daga Janar Buratai

Buratai ya karrama sojojin ne da lambobin yabo a ranar talata da ta gabata domin nuna yabawa ga jarumtar su. Sojojin dai sau biyu mayakan boko haram na kai masu harin ba zata amma a duk Karo biyun sunyi nasara a kan mayakan. Nasarar da sojojin suka samu ta hada da Kama makamai masu dama da suka hada da bama - bamai da motocin yaki a ranar 10 ga watan yuli.

A jawabinsa bayan karrama sojojin, Buratai ya nuna farin cikinsa da nasarar da rundunar sojojin ke samu a kan mayakan, yayi kira ga sojojin dasu kara zage dantse wajen kakkabe ragowar mayakan na boko haram a duk maboyarsu.

Kafin karasawar sa birnin Maiduguri, Buratai yayi sansani rundunar sojoji ta 202 dake Awulari, inda ya shaida gwajin wasu sabbin makamai na yaki da hukumar ta saya.

Buratai ya samu rakiyar shugaban sashen bada horo da zartarwa ta hukumar sojojin, manjo janar David Ahmadu, Ibrahim Attahiru kwamandan Lafiya Dole, manjo janar Ibrahim Manu Yusuf, da wasu manyan sojojin daga shedikwatar soji.

DUBA WANNAN: Shugaba Buhari ne zai lashe zaben shugaban kasa a 2019

Shugaban hukumar sojin na yin rangadin sansanin sojojin ne tun bayan komawarsa da aiki Maiduguri a umarnin da mukaddashin shugaban kasa, Yemi Ysinbajo, ya bayar ga shuwagabannin sojin da su koma Maiduguri da aiki.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a email dinmu na labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng