Samun dama: Kotu ta gurfanar da wata mata akan laifin cin zarafin mijin ta

Samun dama: Kotu ta gurfanar da wata mata akan laifin cin zarafin mijin ta

Daman hausawa sun ce wasu ba su iya cin kwan makauniya ba domin wata mata ta na gasawa mijin ta aya a hannu saboda ya kasance masaki wanda ya janyo mata gurfana a gaban kotu

Wata kotu a babban birnin Abuja ta gurfanar da wata mata, Blessing Igwe mai shekaru 38 saboda gallazawa mijinta da ta ke yi saboda kasancewarsa masaki.

A ranar Larabar da ta gabata ne wannan mata dake zaune a unguwar CBN ta gundumar Apo a birnin Abuja ta gurfana a gaban kotu.

Jami'in dan sanda, Fidelix Ogbobe mai karar wannan mata ya bayyanawa kotu cewa wani mutum Robinson Igwe ya shigar da karar wannan mata a ofishin 'yan sanda na Apo a ranar 2 ga watan Agusta da cewar matar sa Blessing ta na gallaza ma sa ba dare ba rana saboda kasancewar sa masaki.

Samun dama: Kotu ta gurfanar da wata mata akan laifin cin zarafin mijin ta saboda kasancewar sa masaki
Samun dama: Kotu ta gurfanar da wata mata akan laifin cin zarafin mijin ta saboda kasancewar sa masaki

Fidelix ya ce, "matar wannan mutumin ta na ribatar yanayin mijin ta inda ta ke gasa masa aya a hannu don har kwanciyar asibiti ya yi sanadiyar wani rauni da ta yi ma sa a kan sa.

"Duk da shiga lamarin da 'yan sanda su ke yi, hakan bai sa ta daina dukan sa ba"

Ogbobe ya kara da cewa, Robinson ya kai kukan sa ga kwamishinan 'yan sanda na jihar Abuja a kan wannan lamari.

KU KARANTA: An yankewa wata mata daurin shekara 16 saboda ta tsiyayawa saurayin ta soyayyen mai

Ya ce, ta kwashe 'ya'yansu guda biyu kuma ta yi tafiyar ta da su wani wajen da shi kanshi mijin bai sani ba, sai bayan shekara guda ta dawo kuma ta kori mijn na ta daga gidan na su na aure na tsawon kwanaki.

"Mun yi kokarin cafke wannan mata har sau uku inda ta ke guduwa, sai a karo na hudu ne a ka yi nasara"

"Ogbobe ya ce tayi ikirarin kashe mijin na ta ma kuma wannan laifuka ya saba dokar kasa ta sashe na 265, 397 da 172 na final kot."

Har yanzu dai kotu ba ta yanke hukuncin wannan mata ba wanda alkali mai shari'a Alhaji Umar Kagarko ya bayar da belin ta a kan kudi na Naira 20, 000 kuma ya daga shari'ar zuwa 17 ga watan Oktoba.

Don shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng