Kishi kumallon mata: Yaron da kishiya ta yankewa mazakuta ya rasu

Kishi kumallon mata: Yaron da kishiya ta yankewa mazakuta ya rasu

Wani jariri da kishiyar mahaifiyar sa ta yanke ma sa mazakuta ya ce ga garinku nan bayan wata 'yar rashin lafiya da ya gamu da ita

A ranar 18 ga watan Yuni na shekarar da ta gabata ne wani jariri, Dauda Buhari ya rasa mazakutan sa bayan da kishiyar mahaifiyarsa, Bara'atu Rabi'u ta gille ma sa lokacin yana dan watanni biyu da haihuwa.

Shugaba mai kula da kare hakkin yara, Mariam Kolo ta bayyana cewa wannan jaririn ya mutu ne a kauyen Wada da ke karamar hukumar Shiroro dake jihar Neja bayan wata 'yar gajeruwar rashin lafiya ta zazzabin cizon sauro da ya gamu da ita.

A ranar Larabar da ta gabata ne, shugabar ta bayyanawa manema labarai na jaridar PUNCH cewa, "Buhari ya gamu da zazzabin cizon sauro ne inda jikin sa ya dau zafi wanda ya yi sanadiyar mutuwar ta sa bayan an ba shi magunguna."

Kishi kumallon mata: Wata mata ta yanke mazakutar jaririn kishiyar ta
Kishi kumallon mata: Wata mata ta yanke mazakutar jaririn kishiyar ta

Kola ta bayyana cewa Buhari ya cika a daidai lokacin da aka ranar tafiya da shi kasar Ingila domin dashen mazakutar da ya rasa wanda kishiyar mahaifiyar sa ta gille.

KU KARANTA: Yadda Gwamnatocin baya su ka yi wawason kudin wutar lantarki

Ta ce rashin mazakutar ba shine abinda ya janyo ma sa mutuwar ba domin yana cikin koshin lafiya tunda ya samu kulawa daga likitoci da su ka yi ma sa aiki wanda zai rike shi har zuwa lokacin da aka diba na tafiya zuwa kasar Ingila domin yin dashen.

Ta nuna damuwar ta a kan mutuwar wannan jariri wanda a lokacin da ya mutu ya samu shekara guda kenan da haihuwa kuma ta ce har yanzu kishiyar mahaifiyar ta sa ta na nan a tsare a tsohon gidan kaso na Minna dake jihar Neja.

Don shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel