Mummunar cikawa: Ya mutu yayin da yaje kwartanci ɗakin wata mata

Mummunar cikawa: Ya mutu yayin da yaje kwartanci ɗakin wata mata

- Wani mutum ya bar ma iyalinsa abin kunya, bayan ya mutu a dakin wata mata

- Yansanda sun kama matar da magidancin ya mutu a dakinta

Wani magidanci mai mata da yaya ya gamu da ajalinsa a ranar Laraba 9 ga watan Agusta a lokacin gidan wata budurwarsa dake rukunin gidajen kwalejin horar da mayakan Najeriya a babban birnin Abuja.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito Magidancin ya rasu ne bayan daya kammala mu’amala tare da budurwar tasa yayin daya kai mata ziyara da misalin karfe 10 na safiyar ranar.

KU KARANTA: Uwargidar gwamnan jihar Katsina ta kai tallafin magunguna babban asibitin Daura

Rundunar Yansanda jihar ta tabbatar da mutuwar Magidancin bayan da budurwa tasa mai suna Bridget ta kai kara ofishin Yansanda dake Gwarinpa.

Mummunar cikawa: Ya mutu yayin da yaje kwartanci ɗakin wata mata
Wata gawa

Bridget ta bayyana ma yansanda cewar bayan da suka kammala abin da suka saba da Magidancin ne, sai ya tashi ya sanya kayansa, yana shirin tafiya gida, kwatsam sai ya yanke jiki ya fadi matacce.

Sai dai majiyar Legit.ng ta ruwaito a yanzu haka Yansanda sun garkame Bridget, inda suka garzaya da gawar mamacin zuwa asibitin Asokoro don gudanar da bincike akansa, kamar yadda DPO Nurudeen Sabo ya shaida.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Me zaka ce game da neman kudi na yaka halal yaka haram?

Asali: Legit.ng

Online view pixel