Wata mata a Najeriya ta yi kira ga jama'a su taimaka mata da N6.4m don magance cutar nono.

Wata mata a Najeriya ta yi kira ga jama'a su taimaka mata da N6.4m don magance cutar nono.

Wata mace mai shekaru 52 da ake kira Mrs Fehintola Famakinwa, ta yanke shawara ta nemi tallafawa na kudade dan ciwon nonon da ke damun ta.

Misis Famakinwa, wadda ta bayyana cewa ta samu ciwon nonon ne shekaru biyu da suka wuce (2015), an yanke shawarar cewa a nemi kudi domin ta samu cikakken magani.

A cewar Vanguard, ciwon dajin ya riga ya yadu zuwa wasu sassan jikinta, yana barin ta cikin mummunan rauni da zafi.

A kokarin kula da kanta, mahaifiyar 'ya 'ya biyu da ta kasance mai yin abincin sayarwa,ta siyar da duk abin da take dashi, kuma ta kasance a cikin jinƙan abokan makarantar ta da suka ba da gudummawar N1m don magance ciwon ta.

Wata mata a Najeriya ta yi kira ga jama'a su taimaka mata da N6.4m don magance cutar nono.
Wata mata a Najeriya ta yi kira ga jama'a su taimaka mata da N6.4m don magance cutar nono.

Wadda ta kammala digiri a Jami'ar Ibadan ta ce: "Na sani 'yan Najeriya suna da tausayi sosai, kuma na gode musu. Ba na so in mutu. Ina da yara da ke neman kulawa. Ya kamata su taimaka mini don in ci gaba da kula da 'ya'yana, tunda mahaifinsu ya bar mu shekaru da suka wuce. Doctors sun ce ina buƙatar sayan magani wanda za'a yi masa inganci a cikin jinsin chemotherapy hudu da na bari."

KU KARANTA KUMA: Gwamnati tayi watsi da yan kwangilan Najeriya a wajen bada kwangilar layin dogo na kudi har dallan Amurka biliyan 20

Famakinwa wanda ke da hawan jini da kuma ciwon sukari, ta ce ta samu taimako daga mai kulawa inda za ta rinka kashe N10,000 kowace rana.Ta kuma bayyana cewa tana bukatar kimanin N6.4m wanda zai ba da damar biya ma wasu aikin da za'ayi bayan nan kuma wasu matsalolin da zasu biyo baya.

Daya daga cikin 'yan uwanta, Misis Bola Ayanwale, ta shiga cikin rokon' yan Najeriya don su taimake ta, ta kara da cewa Famakinwa zata samu sauki da sauri idan ta samu taimakon gaggawa.

Don shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng