'Yar shekaru 29 ta kashe matarta bayan shekara daya da yin auren jinsi a tsakanin su

'Yar shekaru 29 ta kashe matarta bayan shekara daya da yin auren jinsi a tsakanin su

Wata mata ta harbe amaryarta har lahira a kasar Amurka bayan shekara guda da yin auren jinsi a tsakanin su

Daga kasar Amurka kuma, an samu rahoton cewa wata mata, Laura Bluesstein mai shekaru 29 a duniya ta harbe amaryarta, Felecia Dormans mai shekaru 28 da harsashi na bindiga inda ta aikata har lahira a cikin gidansu na aure dake layin Mill na tsaunin Holly dake garin NewJersey a kasar Amurka bayan shekara guda da yin auren jinsi a tsakanin su

'Yan uwan wannan mata Bluesstein sun kira ofishin 'yan sanda na kurkusa na ofishin Burlington ta hanyar wayar sadarwa su ka labarta mu su wannan al'amari da ya faru.

Nan da nan sai ga jami'an 'yan sanda inda isar su ke da wuya suka riski gawar wannan mata Dormans da harbi a goshinta.

'Yar shekaru 29 ta kashe matarta bayan shekara daya da yin auren jinsi a tsakanin su
'Yar shekaru 29 ta kashe matarta bayan shekara daya da yin auren jinsi a tsakanin su

Laura wadda ita ce a matsayin miji a auren na su ta na cikin gidan a lokacin da jami'an 'yan sanda su ka zo inda su ka cafke ta domin gurfanarwa bayan bincike ya kammala.

Har yanzu 'yan sanda su na bincikar dalilin da ya sa Bluesstein ta harbe matar ta Dormans. Sai dai su na tuhumar ta da laifin kisan kai, amfani da makami mara lasisi da kuma makarar shaida inda su ka tsare ta a ofishin na su na Burlington kuma a ranar litinin mai zuwa za ta gurfana a gaban kotu domin shari'a.

KU KARANTA: Dan Majalisar jihar Legas ya rasa Naira miliyan 9.2 ga gwanayen kwamfuta na shafin sada zumunta

Rahotanni daga shafin su na sada zumunta na Facebook ya bayyana cewa, shekara guda kenan da yin aurensu sannan kuma ya bayyana hotunansu inda suke holewa da shakawatawa kuma har sun bace sun bace na junan su.

Binciken 'yan sanda ya nuna cewa wannan ba shine karo na farko Bluesstein ta aikata laifi ba domin an kama ta miyagun kwayoyi na maye a shekarun 2012 da kuma 2014.

Don shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng