Siyasar Kano: Kabiru Gaya ba dan goyo bane, ya ci amanar Buhari – Inji Kawu Sumaila

Siyasar Kano: Kabiru Gaya ba dan goyo bane, ya ci amanar Buhari – Inji Kawu Sumaila

Mashawarcin shugaban kasa akan harkokin majalisar wakilai Alhaji Suleiman Abdulrahman Kawu Sumaila ya bayyana sanata Kabiru Gaya a matsayin maciyi amanan shugaban kasa Muhamamdu Buhari.

Wani ma’abocin shafin Facebook, Buhari Sallau ne ya daura labarin a shafinsa na Facebook, inda yace Kawu Sumailan ya bayyana haka ne cikin wata hira da yayi da ‘Solacebase’ a garin Kano, inda yace Sanata Kabiru Gaya na daga cikin wadanda ke cin dunduniyar Buhari a majalisa.

KU KARANTA: Wani Fasto yaci kuɗin magada, wata 3 kenan tun bayan daya ranta ana kare, amma fa….

Sumaila yace duk yadda Buhari ke son ganin ya kawo canji , ire iren su Kabiru Gaya ba zasu bari, ind aya bada misalin yadda sanatocin suka yi ma kasafin kudin bana kaca kaca tare da shigar da ayyukan san rai.

Siyasar Kano: Kabiru Gaya ba dan goyo bane, ya ci amanar Buhari – Inji Kawu Sumaila
Kabiru Gaya da Kawu Sumaila

Kawu yace misalin aikin titin Legas zuwa Ibadan an rage shi daga biliyan 30 zuwa 10, haka zalika titin Kano zuwa Maiduguri inda Kabiru Gayan ke wakilta an zaftare kudinsa, inda aka kakkara aikin famfon tuka tuka.

“Duba da zamana a majalisa shekaru 12, babu abinda za’a layance min, a matsayin Kabiru Gaya na shugaban kwamitin ayyuka na majalisar dattawa, yana da rawar da zai taka wajen ganin an tabbatar da kasafin kudin manyan ayyuka, amma yaki, yana gani aka lalata su.” inji Kawu.

Duk kokarin da gwamnati keyi na ganin ta biya ma yan majalisun bukatarsu ta hanyar shigar da ayyukan mazabunsu, bai ishe su ba. Shugaba Buhari nada kudurin yaki da rashawa, amma sai ga shi su Kabitu Gaya ne a gaba wajen rakiyar Sanata Saraki gaban kotu lokacin da ake sharia’arsa.

Dayake mayar da martani, Sanata Kabiru Gaya ta bakin Kaakakin sa, Malam Mustapha Gaya, ya musanta zarge zargen, inda ya danganta su da kokarin bata ma Sanatan suna ne kawai, saboda Kawu na muradin tsayawa takarar kujerar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng