Wike ya bayyana yadda APC za ta murde zaben 2019
-Sun mana alkawarin canji amma bamu ga komai ba
-Sun kara wa yansadan da ake zargin su da murde zabe mukami
-Dimokradiyya ta mutu a Najeriya
Gwamnan jihar Rivas, Nyesom Wike yace jam’iyyar All Progress Congress (APC) sun fara shirye-shiryen murde zaben 2019 ta kara wa yan sandan da ake tuhuma da laifin murde zabe mukami
Wike ya fada haka ne a wani taron lauyoyi a ranar Litinin a birnin Fatakol.
Gwamnan yace hukumar yansanda sun kara wa Mista Akin Fakorede mukami, yanzu shine kwamandan Special Anti-Robbery Squad(SARS) na jihar Rivas, mutumin da aka dauke shi a wani bidiyo yana dukan wani ma’aikacin zabe na INEC.
Wike yace: “Rundunar yan sanda sun kara ma Steve Hasso mukami zuwa assistan commissioner, saboda kokarin da yayi musu na murde zaben 10 ga watan Disamba 2016."
KU KARANTA:Anambra: Ka fara shirin mika mulki - Oyegun ya gaya ma Obiano
“Sun ma yan Najriya alkawarin canji, amma ba mu ga komai ba.
“Dimokradiyya ya mutu a Najeriya. Zuwa 2019 mutane zasu daina maganan dimokradiyya. Sun kara ma Mista Akin Fakorede mukami da ya murde zabe, Mista Stephen Hasso shima gwani ne a murde zabe. Duka sun turo su jihar Rivas ne dan su murde zaben 2019,” Inji Wike.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Bidiyo game da labaran wannan mako
Asali: Legit.ng