Ina mazan ne! Jarumai mata sun fusata, sun bazama farautar Shekau a dajin Sambisa

Ina mazan ne! Jarumai mata sun fusata, sun bazama farautar Shekau a dajin Sambisa

Labarin da muke samu yanzu yana nuni ne da cewa wata tawagar mata yan farauta da kuma maharba sun bazama cikin dazuzzukan dake a yankin Arewa maso gabas domin taimakawa wajen yaki da yan ta'addar Boko Haram.

Ya zuwa yanzu ma dai jaruman sun bayyana cewa su kam yanzu sun riga da sun sadaukar da rayuwar su wajen ganin an kawo karshen wannan ta'addancin da kungiyar nan ta Boko Haram ke tafkawa a yankin nasu.

Ina mazan ne! Jarumai mata sun fusata, sun bazama farautar Shekau a dajin Sambisa
Ina mazan ne! Jarumai mata sun fusata, sun bazama farautar Shekau a dajin Sambisa

Legit.ng ta samu labarin cewa jarumai matan sun bayyana aniyar su ta ba-gudu-ba-jada-baya a kudurin nasu musamman a wannan lokaci da kasar ke fama da matsalolin tsaro kama daga na yan Boko Haram da barayin shanu da ma kwana-kwanan nan kuma masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.

Yanzu haka dai matan na ta ci gaba da samun yabo daga dumbin mutane yan Najeriya musamman ma wadan da ke a yankin da rikicin ya addaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng