Ma’aikatan kamfanin Dangote sun yi masa satan naira miliyan 451

Ma’aikatan kamfanin Dangote sun yi masa satan naira miliyan 451

Wasu ma’aikatan kamfanin siga na hamshakin attajiri Aliko Dangote sun gurfana gaban kotu a ranar litinin 7 ga watan Yuli sanadiyyar tuhumar su da kamfanin ke yi da sata.

Kamfanin dillancin labaru ta ruwaito an gurfanar da ma’aikatan ne gaban babban kotun Ikeja dake Legas, da suka hada da Musa Sule, Joseph Ukpah, Babatunde Ajao, Chinedu Onyekwere, Ezekiel Omoro, Rahman Alayande da Odion Abugba.

KU KARANTA: Sheikh Bala Lau yayi bayani dalla dalla sakamakon cece-kuce da ake yi kan ginin Otal da izala tayi

Majiyar Legit.ng ta ruwaito akwai sauran ma’aikatan su biyu da a yanzu haka hukumar tsaro ke nemansu ruwa a jallo, da suka hada da Zainab Adebanko da Mannir Mohammed.

Ma’aikatan kamfanin Dangote sun yi masa satan naira miliyan 451
Kamfanin Siga

Bugu da kari cikin wadanda ake tuhumar har da Habib Mande da kamfaninsa El-Habib Property Nigeria Limited, dukkaninsu ana tuhumar su ne akan laifuka 8 da suka hada da hadin baki, sata, da kuma hada takardun bogi.

Lauya mai kara ya tabbatar da cewa mutanen sun aikata laifin ne a tsakanin shekarun 2012 da 2016 a kamfanin sigar dake Apapa, inda yace Mande ne yayi amfani da kamfaninsa wajen satar siga na naira miliyan 451 tare da hadin bakin ma’aikatan kamfanin.

Sai dai wadanda ake tuhumar duk sun musanta zarge zargen, daga nan sai alkali mai shari’a Sedotan Ogunsanya ya dage sauraron karar zuwa 22 ga watan Satumba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng