Masu mata fiye da 1 sun fi nisan kwana a duniya - Bincike

Masu mata fiye da 1 sun fi nisan kwana a duniya - Bincike

Wani sakamakon binciken da masu binciken kimiyya suka gabatar a kasashen duniya sama da 140 ya bayyana yadda auren mata fiye da 1 ke taimawa mazaje wajen dadewa a duniya.

An dai bayyana wannan rahoton binciken ne dai a yanar gizo inda ya bayyana tare da hujjoji da kuma karin bayanan masana yadda auren mace fiye da daya ke ka karawa mazaje daga al'ummomin dake auren mataye fiye da daya tsawancin kwana.

Masu mata fiye da 1 sun fi nisan kwana a duniya - Bincike
Masu mata fiye da 1 sun fi nisan kwana a duniya - Bincike

Legit.ng ta samu cewa haka nan ma wata malamar sanin rayuwar dan adam a jami’ar Sheffield da ke Birtaniya mai suna Birpi Lummaa ta ce, sakamakon binciken da suka yi a kasashe 140 ya nuna musu mutane kimanin 60 daga kasashe masu auren mace fiye da daya suke samun karin shekarun da suka kai 12 na rayuwar su fiye da wadan da wadan da basu auran mace sama da daya.

Addinin musuluci dai ya amince wa mazaje da su auri matan da suka kai hudu idan har suna da iko kuma sun tabbatar da za su yi adalci a tsakanin su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng