Kwankwaso ne kadai zai iya dawowa da martabar Arewa a Najeriya - Aminu Ala

Kwankwaso ne kadai zai iya dawowa da martabar Arewa a Najeriya - Aminu Ala

Shahararren mawakin nan na Hausa kuma mai tarin hikima da sani a harshen Hausa da adabi watau Aminu Ala ya bayyana tsohon Gwamnan Kano kuma Sanata a yanzu Alhaji Rabi'u Musa Kwankwaso a matsayin mutum daya tilo da zai dawo da martabar arewa a Najeriya.

Aminu Ala yayi wannan bayanin ne a cikin wata fira da yayi da makilin majiyar mu Rariya inda yace yana da yakinin cewa Kwankwaso zai dawo da martabar arewa da kuma maido mata da dukkan damar da take da ita da ta rasa.

Kwankwaso ne kadai zai iya dawowa da martabar Arewa a Najeriya - Aminu Ala
Kwankwaso ne kadai zai iya dawowa da martabar Arewa a Najeriya - Aminu Ala

Legit.ng ta samu cewar dai shahararren mawakin ya kuma ce: "Kwankwaso mutum ne wanda bai da tsoro kuma zai iya taka tuk wanda ya yi mai gani-gani, ba tare da shakku ba."

Ala ya ci gaba da cewa shi a ganin sa ko wannan tada kayar bayan da yan yankin Biafra ke yi ba zasu iya yin ta ba idan yana mulki. Haka ma kuma Kwankwaso a cewar Aminu Ala yana son gida sosai don ko a Kano yafi son karamar hukumar sa ta Madobi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng