Sojoji sun hallaka wani kwamandan Boko Haram (Hotuna)
- Sojoji sun hallaka wani kwamandan yakin Boko Haram
- An kwato dimbin makamai daga hanneyen mayakan Boko Haram
Rundunar Sojojin Najeriya sun hallaka wani kwamandan Boko Haram biyo bayan wani karanbattan da suka yi a ranar Lahadi 6 ga watan Agusta, kamar yadda wani kwamandan Sojojin sa kai ya bayyana.
Kwamanda Mu’azu Alhaji Misiya ne ya daura hotunan kashe kashe da suka yi ma Boko Haram tare da barnar da suka yi musu, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.
KU KARANTA: Ta’addanci: Hukumar ‘yan sanda ta bayyana dalilin da yasa aka kai hari a cocin Katolika a Anambra
Cikin kayayyakin da Sojojin suka kwato sun hada da bindigu guda 2, alburusai da kuma wata babbar motar yaki na yan Boko Haram.
A wani hannun kuma, babban hafsan sojan kasa laftanar janar Tukur Buratai ya isa jihar Borno yankin Arewa maso gabashin kasar nan, bayan umarnin da mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya bashi.
Ga sauran hotunan:
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Kalli bidiyon yadda Sojoji ke aman wuta akan yan Boko Haram:
Asali: Legit.ng