'Yan mata 145 ne 'yan Boko Haram suka yi amfani dasu wajen kunar bakin wake a bana
- Mayakan Boko Haram sunyi karanci, don haka sun koma kashe 'marayun yara mata a kunar bakin wake
- Da yawa basu iya ciyar da su ne, kuma yaran basu so, amma ana tilasta musu
- Rashin tausayin Boko Haram ya kai har mai ciki da mai goyo suna turowa
A kididdigar da jaridar Punch Nigeria ta fitar a karshen makon nan, an ruwaito cewa kungiyar Boko Haram tayi amfani da akalla 'yan mata 'yan kunar bakin wake 145 daga farkon banan nan. Wannan baya kirgawa da na gari da jama'a basu kai rahoto, da ma na kauyuka da basu kusa da jama'a.
A kirgen dai, wanda aka hado daga jami'an soji, da na 'yansanda, da na kungiyar Civilian JTF, da ma ta NEMA an gano cewa kungiyar ta kara kaimi wajen amani da mata kanana, masu ciki, masu goyo, da ma kanana, wadanda basu ji ba basu gani ba.
A watan Janairu dai mata 15 ne suka rasu ta wannan hanyar, 10 a Fabrairu, sha biyar a watan Maris da Afrilu da Mayu, sai talatin a Yuni, da talatin a Yuli, lokacin azumi kenan, wanda kungiyar kan kara kaimi wai neman falalar wata mai tsarki.
DUBA WANNAN: Sanatocinku da suka yin aiki a shekaru 3 bayan zabo su
A dai tasu fahimtar, Boko Haram na ganin yaran suna bukarar su mutu, saboda suyi rayuwa mai dadi a aljanna, domin kada a karar da mayakan, matan su yi karatun boko daga baya, ko ma su auri mutanen gari wadanda suke gani duk kafirai ne da zasu kaisu ga wutar jahannama.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a email dinmu na labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng