Bincike kan wai ko kabilar Ibo suna da alaka da kabilar Yahudawa

Bincike kan wai ko kabilar Ibo suna da alaka da kabilar Yahudawa

Misalin watanni 5 da suka wuce, Legit.ng ta bada rahotan cewa wasu masu binciken kimiya na kasar Israela sun ziyarci garin Nnewi da ke jihar Anambra domin gudanar da bincike akan ikirarin cewa asalin yan kabilar ibo daga can israela suke, toh yanzu masu binciken sun dawo.

Har ila yau, Legit.ng ta taba kawo rahoton ziyarar da masu binciken kimiyan israila suka kai zuwa asibitin tsohon direkta kuma shugaban kungiyar Ohanaeze Ndigbo, Dr Dozie Ikedife duk dai saboda suyi bincike akan sinadarin gina rayuwa na 'DNA' a turance Deoxyribonucleic Acid da ka iya nuna musu idan akwai alaqa ta jini tsakanin kabilar ibo da mutanen israela.

Toh, yanzu dai masu binciken kimiyan sun dawo garin Nnewi da sakamakon binciken da sukayi akan sinadarin na DNA da zai warware wannan muqaballar. Masu binciken kimiyan sun taho ne karkashin jagorancin shugaban wata kungiya mai suna Jewish voice ministries.

Shin asalin kabilar ibo yan israela ne? Masu binciken kimiya na isreala sun zo Anambra domin warware abin

Wannan ziyarar tasu itace na hudu zuwa garin Nnewi din domin kawo sakamakon binciken da sukayi wanda rahotanni suka ce tabbas mutanen kabilar ibo da ke kudu maso gabashin Najeriya suna da alaqa da mutanen kasar Israela.

Shin asalin kabilar ibo yan israela ne? Masu binciken kimiya na isreala sun zo Anambra domin warware abin
Shin asalin kabilar ibo yan israela ne? Masu binciken kimiya na isreala sun zo Anambra domin warware abin

Rahotanni sun ce shugaban rikon kwaryar kwamitin Nnewi ta arewa, Prince Chukwudi Orizu ne ya tarbe su a Messianic Faith Assembly a Uruagu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a email dinmu na labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel