Ankama dan Njaeriya a Amurka da aikata laifin zamba da yaudara a yanan gizo

Ankama dan Njaeriya a Amurka da aikata laifin zamba da yaudara a yanan gizo

-Yashiga kasan Amurka da Visan ziyara

-Ankama shi da laifin zamba da sata.

-Hukuma ta gargadi mutune da game da barayin yanan gizo

Hukumar Bincike ta FBI ta kama wani dan Najeriya mai suna Daniel Ojo da yayi watanni 14 a kasan Amurka da aikata laifin zamba da sata.

Mr Ojo yana amfani da yana gizo ne wajen cutar mutane. Musamman masu aiki a makaratun dake garin Connecticut da Minnesota.

Kamfanin dillancin labarai na kasar Sin, Deirdre Daly, da Babban Jami'in Jakadancin Amurka na Connecticut, Patricia Ferrick, ya bayyana a ranar Jumma'ar da ta gabata a ka samu nasarar kama Mr Ojo.

Ankama dan Njaeriya a Amurka da aikata laifin zamba da yaudara a yanan gizo
Ankama dan Njaeriya a Amurka da aikata laifin zamba da yaudara a yanan gizo

Bayan an kama shi a gidan shi dake unguwan Durham, Mr. Ojo ya bayyana a gaban babban alkalin kotun Amurka dake Greensboro, N.C., kuma alakalin y aba da umarnin tsare shi har sai an kamala Bincike.

KU KARANTA: Gwamna Ganduje ya sake jaddada kudurin hadin kan kasa

Hukumomi a Amurka sun ce Mr. Ojo ya shiga kasan ne a watan Mayu 2016 da visan ziyara kuma ya ki koma wa kasar sa da visan ya kare tun a watan Yuni 2016.

Mista Daly ya bukaci jama'a su sake duba shafuka da adiresoshin imel kafin dannawa da amsawa dan su, kubuta daga hannun barayin yanan gizo.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng