Bincike ya nuna kusan kashi 9 bisa goma na likitocin Najeriya na kokarin tserewa aiki Turai

Bincike ya nuna kusan kashi 9 bisa goma na likitocin Najeriya na kokarin tserewa aiki Turai

- Albashin likitoci a kasashen waje yafi tagomashi

- Likitoci na tserewa waje domin Najeriya ba kudi a aikin

- Ana karancin likitoci a kasa Najeriya

A wani bincike da aka yi ya nuna sama da rabin likitocin Najeriya suna kokarin tserewa kasashen waje aiki. Rashin ingantattun asibiti, rashin kayan aiki, da albashi mara yawa sun sa likitocin Najeriya da yawa suna neman aiki a Turai.

A bisa binciken, kasar Amurka da Ingila sune manyan kasashe da likitocin Najeriya suke neman aiki. Saboda haka da yawa daga likitocin Najeriya sun yi rijistar rubuta jarabawar kasar waje ta zama likita kamar su PLAB ta Ingila, USMLE ta Amurka, MCCE ta Canada, AMC ta Australia da DHA ta Dubai.

Bincike ya nuna kusan kashi 9 bisa goma na likitocin Najeriya na kokarin tserewa aiki Turai
Bincike ya nuna kusan kashi 9 bisa goma na likitocin Najeriya na kokarin tserewa aiki Turai

Wani ma’aikaci dan kungiyar Residnt Doctors Dr. Abimbola Olajide ya bayyana a tsakanin ‘yan kungiyarsu sama da likitoci 2,500 zasu bar Najeriya zuwa kasashen waje don neman samun cigaba a rayuwarsu.

Karin bincike daga NOIPolls ya nuna dalilin da yasa ake samun raguwar ma'aikata a yankin kiwon lafiya sun hada da kalubalen da ake fuskanta daga yawan haraji da ake cira daga albashi, karancin gamsuwa da aiki, albashi mara wadata, da tazarar da ilimin likitanci yayi a kasar waje kwatankwacin na Najeriya.

Rahoton ya nuna wannan sune manyan matsaloli daga binciken da aka yi, da fatan wannan binciken zai ta da masu ruwa da tsaki tsaye a yankin kiwon lafiya, zai kuma jawo gyaran da ake bukata a yankin kiwon lafiya.

DUBA WANNAN: Sanatocin da basu yo doka ko daya ba tun 2015

Manyan da suka halarci taron sun yi magana cewar gwamnatin tarayya da ta jihohi suna bukatar daukar babban mataki akan lamarin don ya zama abin da yake neman dubiya da gaggawa kar ya zama abin kunya ga kasa.

Najeriya tana da likitoci 72,000 da suka yi rijista da 'Medical and Dental Council of Nigeria' amma likitoci basu fi 35,000 da suke aiki a kasar ba. Barin likitoci daga Najeriya ya zama babbar matsala da kasa take fuskanta.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a email dinmu na labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel