Wata mata ta tara N700,000 don taimakawa mai gidanta, shin sana'a ta fara? Ko aure ya karo?
- Wata mata ta tara kudi a asusu don taimakawa mai gidanta ta fara sana'a
- Ta dauki tsawon wata 7 tana tana kudin a asusu
- Tana kira ga mata suyi koyi da ita ba sai sun jira mai gidansu ya tallafa musu ba
Kun taba tunanin fara sana’a amma daga baya sai ku ajiye ra'ayin saboda rashin jari? Labarin wannan matar zai kara muku karfin gwiwa ku fara tara jari wajen sana'a.
Wata mata ‘yar Najeriya ta fadi anfanin tara kudi yayin da wata kawarta matar aure ta tara N700,000 a asusu. Matar mai suna Peace Ijeoma a dandalin Facebook ta nuna yadda kawarta ta tara kudin da kadan-kadan.
Ta dauki har tsawon wata bakwai tana tarin, bayan ta fasa asusun ta lissafa kudin da ta tara ta ga ya kai N700,000. Matar ta tara ne don ta bawa mijinta mamaki ta fara sana’a da kudin.
Matar ta samu labarin tara kudi a asusu ne, tace itama bari ta gwada. Ta fara tarin daga N500 da N1000 a kudin da ya kamata ta sayi kati da sauran abubuwa, amma sai ta yanke shawarar barin siyan su ta tara kudin a asusu.
KU DUBA: Ganawar Buhari da Osinbajo tsawon minti 40 a Landan
'A watan Disamba ta fara tarin, yanzu haka ta tara N700,000. Tayi niyyar anfani da kudin don ta fara sana’a, hakan zai ba mijinta mamaki ganin ta tara kudin.'
'Wannan hotunan da ta turo don wasu suyi koyi da hakan ne musamman ma matan da suke gida da basa sana’, ba sai sun jira mai gidansu ya bude musu hanya ko ya basu jarin sana’a ba.'
'Akwai abubuwa da yawa da zaka yi su taimake ka, musamman tara kudi a asusu, da fara sana'a da jari kadan kafi ta kai babba.'
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a email dinmu na labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng