An maka wani gardi gaban kotu kan yi ma ƙaramar yarinya fyaɗe a jihar Kano

An maka wani gardi gaban kotu kan yi ma ƙaramar yarinya fyaɗe a jihar Kano

- Rundunar Yansandan jihar Kano ta shigar da wani matashi dan fyade kara

- Alkalin kotun ya bukaci a daure masa shi a gidna yarin Bichi

Rundunar Yansandan jihar Kano ta tasa keyar wani matashi mai suna Ibrahim Musa mai shekaru 25 gaban wata kotun majistri dake jihar kan zarginsa da haike ma wata karamar yarinyar yar shekara 9.

Yansanda sun kama Musa ne da laifin yi ma wannan yar talla fyade yayin da take aikinta na tallar Masa a kauyen Saje na garin Bichi, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA: Badaƙalar gidan N700,000,000: Sheikh Gumi ya caccaki mai alfarma Sarkin Musulmi

Sai dai mai shari’a Muhammad Jibril ya bukaci a garkame masa wanda ake tuhuma a kurkuku har sai ranar 10 ga watan Agusta don cigaba da sauraron karar.

An maka wani gardi gaban kotu kan yi ma ƙaramar yarinya fyaɗe a jihar Kano
Wata yarinya

Da fari, sai da dansanda mai kara ya shaida ma kotu cewa wani mutumi mai suna Bashir Ado ne ya kawo karar Musa, inda yace “Ya yaudari yarinyar har ya shigar da ita shagonsa dake, kuma ya tursasa mata saduwa da shi.”

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Dansanda mai kara, Inspekta Pogu Lala yana fadin wannan laifin yaci karo da sashi na 283 na kundin Final kod.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel