An sallamo mutane 100 daga gidan kurkukun Kiri Kiri na jihar Legas
Hukumar kula da gidajen yari ka kasa ta sallamo mutane 100 dake tsare a gidan Kurkukun Kirikiri a ranar Alhamis a wani tsari na rage cunkoson mutane a gidajen yarin kasar nan.
Kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito shugaban hukumar reshen jihar Legas yana fadin cewar sun saki mutanen ne a kokarin sun a rage cunkoson mazauna gidan yarin, sa’annan yace dukkaninsi masu kananan laifuka ne.
KU KARANTA: Jami’an Ýansanda sun yi carafken cafke ɓarayin dake satar mutane a Kaduna (Hotuna)
Kwantrola Tunde Oladipo yace yawancin mutanen da aka kama an kama su ne suna kasuwanci akan tituna da kuma yawon dare, inji majiyar Legit.ng.
“Wani attajiri ne ya rubuto mana yana son ya samar ma mazauna gidan yarin abinci, amma sai na shawarce shi daya sama masu yanci ba abinci ba, kuma ya yarda ya biya musu tarar da aka sanya musu.” Inji Kwantrola Tunde.
“Gaskiya mun ji dadin zuwan wannan bawan Allah daya nemi in sakaya sunansa, saboda dama muna fama da cunkoson mutane a cikin kurkukun.” Ya cigaba da fadi.
Daga karshe ya shawarci mutanen da aka sallama da su guji zuwa inda ake aikata miyagun laifuka, sa’annan ya bukaci dasu dage wajen sana’ar da zata rike su. shima wakilin attajirin, Fasto Taiwo yace zasu horar da matasan sana’o’i.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Yadda Yansanda suka kama kasurgumin barawon mutane, Kalla:
Asali: Legit.ng