Amana tayi wuya: Yadda wani Maigadi ya arce da dukiyar Maigidansa
- Kotu ta yanke ma wani Maigadi daya sace kayan Maigidansa
- Maigadin ya sace kaya ne daga shagon da aka amince masa yayi gadi
A ranar Alhamis 3 ga watan Agusta ne aka gurfanar da wani mutum mai suna Vincent Anyaegbu gaban kuliya manta sabo kan tuhumarsa da ake yi da ha’intar Maigidansa N655,000.
Dansanda mai kara ya gurfanar da matashin mai shekaru 25 ne gaban kotun majistri dake garin Ikeja jihar Legas, inda dansandan, Sajan Godwin ya bayyana ma kotu cewar wanda ake zargin ya aikata wannan halin bera ne a watan Yuli.
KU KARANTA: An shiga ruɗani yayin da direbobin ‘a-daidaita-sahu’ suka tare hanyar shiga fadar gwamnati
“Mutumin ya sace kwalaben siyarwa ne guda 28,800, wanda jimillan darajarsu ta kai N655,000, inda sai bayan da aka nemi kayan aka rasa ne, sai aka lura shima Maigadin ya tsere.” Inji dansanda.
Sai dai maniyar Legit.ng, kamfanin dillancin labaru, NAN ta tabbatar wannan laifi yaci karo da sashi na 287 na kundin hukunta miyagun laifuka na jihar Legas, amma mutumin ya musanta zargin.
Daga nan sai Alkalin kotun ya bada belin wanda ake zargin kan kudi N50,000, tare da dage sauraron karar zuwa ranar 30 ga watan Agusta.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng