Kashi 25 ne bisa 100 na matan Najeriya ke shayar da ya’yan su Nono har na tsawon wata 6

Kashi 25 ne bisa 100 na matan Najeriya ke shayar da ya’yan su Nono har na tsawon wata 6

A bisa ga bincike kungiyar dake kula da yara kanana na majalisar dinkin duniya, ta bayyana cewa iyaye mata da dama na Najeriya kaso 25 cikin 100 kadai ne ke shayar da yaransu nono har tsawon wata shidda.

Jami’in hukumar Stanley Nanama ya bukaci mata da su mayar da hankali sosai wajen shayar da yaransu domin hakan na da matukar muhimmanci ga lafiyar yaran.

Ga wasu daga cikin muhimmancin shayar da yara nono na tsawon wannan lokaci:

1. Ruwan nono nada muhimmanci wajen hana mutuwar yara da zaran an haife su

2. Yana kara kuzari ga lafiyar yaro ta yadda zai girma kamar yadda ya kamata

KU KARANTA KUMA: Dalilin da ya sa na fito a Barauniya – Hafsa Idris

3. Hakan ya na ba yaro kariya daga kamuwa da cututtukar fata da sauransu

4. Haka zali su kansu iyaye mata hakan na taimakawa wajen basu kariyaa daga cutar daji na mama

5. Daga karshe rowan nono na sa yaro ya kasance mai kaifin basira da tunani

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng