Yadda Fastoci suka sa karuwa a mutuwar mata masu ciki - Kwamishinan Cross River
kwamishinan kiwon lafiya na Cross-river, Inyang Asibong, ta ce cewa kara yawan adadin mutuwar mata masu ciki na saboda Fastoci wanda suke sa su zuwa kungiyoyin Imani (FBOs)
Asibong ta bayyana haka yayin da ta idar da wata Jigon lacca a 2017 a wani gamuwa da taron harkokin kimiyya na Jihar Cross River babi na Jam'iyyar likitocin Nijeriya inda ta ce cewa jihar zata dau matakai don komar da hankalin mazauna ga likita.
Ta ce: "Muna da shugabannin addini da suke gaya wa wadannan mutane abin da za su yi, kuma sun fi son sauraron su fiye da iyayensu ko ma'aikatan kiwon lafiya.
"Mafi yawa sun fi son suyi nakuda mai tsawo,sa'annan sai sun kasa sai suje asibiti a lokacin da suka numfashin karshen su. A ƙarshe lokacin da suka mutu a asibiti,ba za mu iya kama su ba,saboda ba su yarda saboda wayanda ake magana akai fastoci ne,shikenan an barsu sun tafi . "
Ta ce wannan matsalolin za a sha kansu ta hanyar gina cibiyoyin shawarwari, wadda za a iya amfani da dalilai na shiga tsakani don hana sake faruwar abin.
"Muna kokarin warware al'adar ta yin amfani da kiwon lafiya da bayar da cibiyoyin shawarwari da kuma magana da fastoci jahilai,da su bari marasa lafiya su je asibitoci inda za su iya ko da yaushe zuwa da addu'a a gare su," In ji Dr. Asibong.
KU KARANTA KUMA:Bambancin siyasa ya sa Gwamnatin Jihar Kaduna za ta rusa ginin wani Sanata?
Har ila yau, ta nuna cewa, farkon ganewa na cututtuka da kuma kiyaye wa shi ke kayo lafiya mafi yawa ga dan Adam.
Ta ce cewa: "Saurin gane cutar da kuma rigakafin ne mafi alheri ba magani ba. Idan muka jira har cutar ta cigaba, za mu sami wata matsala wurin warkar da wannan mutumin.
"Dauki misali ciwon daji, ba mu da isasshen kayan aiki da zamu iya kiwor dashi, amma idan cutar sankarar mahaifa ne aka gano tun farkon, shi za a iya gaba daya warkar dashi."
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng