Zantawa: Yanda na samu gayyata zuwa sayan kayan gidan tsohon shugaban kasa Jonathan-Dan kasuwa

Zantawa: Yanda na samu gayyata zuwa sayan kayan gidan tsohon shugaban kasa Jonathan-Dan kasuwa

-Yan sanda sun yaudare ni

-Dole mutu yayi takatsantsan da yansanda

-Na gudu ne sabo kunyan da nakeji na siyan kayan sata bisa Kuskure

Dan jaridan PREMIUM TIMES ya zanta da wani dan kasuwa mai suna Ibrahim Bagobiri, ciyaman din masu sayan kayan hanu dake kasuwan Tipper Garage Abuja. Ya bayyana yadda wasu suka yaudare shi har suka shi ya saya kayan gidan tsohon shugaban Jonathan da suka sace.

DJ: Menene sunan ka?

IBRAHIM: Sunana Ibrahim Bagobiri, amma am fi sanina da ciyaman din kasuwan Tipper Garage.

Zantawa: Yanda na samu gayyata zuwa siyan kayan gidan tsohon shugaban kasa Jonathan-Dan kasuwa
Zantawa: Yanda na samu gayyata zuwa siyan kayan gidan tsohon shugaban kasa Jonathan-Dan kasuwa

DJ: Kasan wani dan sanda mai suna sajent Musa?

IBRAHIM: Nasan sajent Musa sosai kuma shi ma ya san ni. Mun san juna na tsawon shekara 12. Yana yawan zuwa kasuwan mu.

KU KARANTA:'Yan sanda sun kama makafi biyu da suke bara a jami'ar kasar

DJ: Ya akayi ka shiga ciniki da shi?

IBRAHIM: Nagode. Komai yafara ne tun a shekaran 2016, kafin a fara azumin Ramdan na shekaran. Wani matashi ya tunkare ni a matsayin dan aiken sajent Musa.

Matashin ya zo mun da tufafi kala shida yace mun Musa yace na saya saboda ya kaima sa kudin. Naji mamaki da naji haka saboda bamu ta ba kasuwan ci da juna ba.

Sai nakira wayar sa da sauri na tambaye shi. Musa ya tabbatar mu da cewa ba kayan sata bane ogansa (Jonathan) ya bashi kyauta.

Da nuna mishi ba zan iya saya ba, sai yace mun wato na dauki shi a matsayin barawo kenan.

Ya dauke su kwana biyu kafin suka shawo kaina har na saya kayan. Bayan haka sai suka gayyaci ni gidan, suka nuna mun cikin wani daki da aka ajiye kaya daywa.

DJ: Ka kara siyan kayan da suka nuna maka?

IBRAHIM: A’a bari na kai ka baya. Kafin nashiga gidan wani dan sanda yace mun, za su kai ni wani dakin da ake ajiye kaya dayawa Jonathan ya raba musu kyauta bayan sun fadi zaben 2015.

Da nashiga dakin sai naga wani zannen Jonathan mai kyau a bango . yadda naga wajen zuciya ta ta raya mun babu yanda zai yiwu a basu masu tsaro irin wannan kyautan

Da su lura na tsorata, su suka ce mun kada na damu. Sai na kale fuskokin sun ace ‘Musa, ko za zama wanda yafi kowa kudi a Najeriya ta kayan nan b azan saye sub a.

Haka dagantaka na da Musa ta kasance kafin yafara neman wasu masu saye.

DJ: An tabbatar da cewa a kasuwan tipper Garage aka sayar da sauran kayan?

IBRAHIM: Gaskiya ne. Dana daina saya kaya a wajen su sai suka fara sayar ma wasu yan kasuwan.

DJ: Mai yasa baka dauki mataki ba da ka gano kayan ba na kyauta bane daga Jonathan?

IBRAHIM: Baka san ni bane shi yasa kake mun wannan tambaya. Idan kana hulda da yansanda mussaman matsala irin na kayan sata dole kaya takatsantsan.

DJ:Mai yasa ka gudu?

IBRAHIM: Na gudu ne ba dan ina tsoro ba. Na gudu ne saboda kunya da nake ji na sayan kaya sata bisa rashin sani. Kowa ya sanni kusa kuma siyan kayan sata yana cikin dokar mu na kasuwaIdan muka gano wani yazo sayar da kayan sata muna kama mai laifin ne mu damka wa hukuma.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Don shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel