Wani jariri da aka haifa ɗauke da juna biyu ya baiwa likitocin duniya mamaki (Hotuna)

Wani jariri da aka haifa ɗauke da juna biyu ya baiwa likitocin duniya mamaki (Hotuna)

Wata budurwa mai shekaru 19 ta haifi jariri wanda yazo da wani abin mamaki da ba’a saba ganinsa ba, shi dai wannan jariri haihuwarsa aka yi da juna biyu, inji rahoton Daily Trust.

Likitoci sun tabbatar da cewa wannan jariri da aka haifa a kasar Indiya, yazo tare da dan uwansa yan biyu, amma yan biyu yana zaune ne a cikin cikin wannan jariri.

KU KARANTA: Saurayi ya hallaka budurwarsa kan tana zance da tsohon saurayinta

A farkon watan Yulin bana ne aka fara lura da wasu kasusuwan halitta a cikin cikin wannan jariri, kamar yadda likitocin suka ce:

Wani jariri da aka haifa ɗauke da juna biyu ya baiwa likitocin duniya mamaki (Hotuna)
Jaririn

“A hoton bayan haihuwa da muka yi ma jaririn ne muka tsinkayi wata halitta ta rabin mutum hade da kwakwalwa, kafafu, da hannuwa cikin wata karamar mahaifa a cikin sa.

“Ba shakka yan biyu matar nan ta haifa, amma dayan jaririn na cikin jaririn da aka haifa, inda shi daya jaririn sati 13 kawai yayi yana girma, daga nan sai ya daina girma.” Inji likitan mai suna Thorat.

Wani jariri da aka haifa ɗauke da juna biyu ya baiwa likitocin duniya mamaki (Hotuna)
Likitocin tare da jaririn

Bayan haihuwar wannan jariri ne a ranar 20 ga watan Yuli a asibiti dake kusa da Mumbai sai aka gudanar da aikin tiyata akan sa, inda aka cire masa wannan yan biyu nasa, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.

Wata likitan mata a asibitin, Neena Nichlani tace sau 100 kacal aka taba samun irin wannan haihuwa a duniya gaba daya, inda ake samun irinsa gida daya a duk cikin haihuwa 500,000.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel